 |
|
 |
This is Islam |
|
| Yana daga cikin musulunci |
ka yi imani cewa wannan duniyar da abin da ke cikin ta akwai wanda ya halicce su, shi ne Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya, ya daidaita a sama, yana sane da abin da halittu ke aikatawa, yana ganinsu, kuma yana jinsu. Shi kadai ya cancanta a bauta masa, ka bar bautar wanin Allah. Kuma kayi imani lallai Allah madaukakin sarki bai halicci mutane ba domin wasa, kadai ya halicce su ne domin su bauta masa kuma da sannu zai tashe su wani lokaci ranar alkiyama, domin a yi musu hisabi akan ayyukan da suka yi a duniya |
|
|
|
| Yana daga cikin musulunci |
ka yi imani cewa Allah Madaukakin Sarki yana da mala'iku wanda sun sha banban da mutane, ba ma ganinsu, Allah ya halicce su ne daga haske, kuma ya jibinta musu wasu ayyuka, daga cikinsu akwai: mala'ika Jibril, wanda Allah ya jibinta masa isar da wahayi zuwa ga annabawa |
|
|
|
| Yana daga cikin musulunci |
ka yi imani cewa Allah madaukakin sarki ya saukarwa Annabawa littattafai misalin Attaura, Injila, Zabura. Na karshansu shi ne Alkur'ani wanda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kuma dukkanin wadannan littattafan su na umarni ne da a bautawa Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya. To bayan shudewar lokaci canje canje sun shiga wadannan littattafai daga bangaren makiya addini wadanda suke cin dukiyoyin mutane ba tare da hakki ba. Amma Alkur'ani wanda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne kadai wannan canjin bai shafa ba, domin shi Allah ya dauki nauyin kare shi daga canji ko bacewa, kuma Allah ya sanya shi ya zamo mu'ujiza ne ga 'yan adam, sannan kuma ya zamo abin kiyayewa ne ( hadacewa ) a zukatan mazaje. Kuma Allah ya sanya shi mai shaida kuma mai hukunci ne akan littattafan da suka gabace shi. Sannan kuma yana kunshe da mu'ujizozi wadanda malaman wannan zamanin suka yi shaida a kai

|
|
|
|
| Yana daga cikin musulunci |
ka yi imani cewa Allah madaukakin sarki ya halicci Annabi Adam ne daga kasa, kuma shi ne farkon 'yan adam a ban kasa, sannan kuma ya halicci sauran 'yan adam daga gare shi domin ya jarrabe su. Bayan shudewar wani lokaci sai mutane suka bata kuma shaidanu suka halakar da su, suka bautawa gumaka. Sai Allah ya aiko da manzanni daga cikin mutane su isar musu da sakon Ubangiji, shi ne bautar Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya, da kuma bin manzanni, tare da barin bautar wanin Allah. Daga cikin wadannan Annabawan akwai: ( Nuhu, Ibrahim, Musa, Isa, da sauransu) na karshansu shi ne Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma shi ne cikamakin Annabawa. Musuluncin mutum ba ya inganta har sai ya yi imani da dukkan Annabawan Allah kuma ya so su. |
|
|
|
| Yana daga cikin musulunci |
imani da cewa duk wani abu da yake faruwa a wannan duniya Allah ne Ya kaddara shi. Kuma Allah Ya riga Ya rubuta shi tun gabanin ya faru. Tare da cewa shi dan Adam an umarce shi da ya yi riko da sababbai, kuma shi ne wanda zai yi aikin da kansa, sannan shi ne zai jibinci duk wani sakamakon aikinsa a nan duniya da kuma lahira. Bai halatta gare shi ba ya bar aiki ya yi hujja da kaddara. To akida irin wannan za ta sanya ka ka rayu cikin kwanciyar hankali. |
|
|
First 1 2 3 4 5 Last
|
|
 |
Main Menu |
|
|
 |
|
| |
Languages |
|
 |
|
|
 |