Shafin Farko
Library
Related sites
About Us
Contact us
_IyHAqoaspsitu
Name
Email

_LATEST_BOOK
RUKUNAN IMANI
Introduction to Islam in Hausa Language
RUKUNAN MUSULUNCI
Prayer
 
Musulunci

yana umartarka da ka yi sallah kamar haka

 1. Ka fuskanci Alkibla sannan ka ce:  (Allahu Akbar) ka na mai daga hannayanka daf da kunnuwanka sannan ka dora hannunka na dama akan hannunka na hagu sai ka
dora akan kirjinka sannan ka karanta fatiha
sai kace :

        

lBismillaahir- Rahmaanir- Raheem . Al- hamdu  lillaah Rabbil alameen. Arrahmanir Raheem. Maaliki yaumiddeen. Iyyaaka na'abudu wa iyyaaka nasta'een. Ihdinas-Siratal Mustaqeem. Siratal lazeena an'amta alaihim ghairil Maghdhubi alaihim waladdhaleen. Ameen.

Ma'ana: (Da Sunan Allah Mai Rahama Mai-jin-kai. Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Mai rahama , Mai jin kai . Mai nuna Mulkin Ranar Sakamako . Kai muke bautawa kuma Kai muke neman taimakon ka . Ka shiryar damu ga hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Ka yiwa ni'ima , ba wadanda Kayi wa fushi ba , kuma ba batattu ba) .
Sannan sai ka karanta abin da ya sauwaka daga cikin Alkur'ani kamar Suratul-Ikhlas:

Ma'ana: (Da Sunan Allah Mai Rahama Mai-jin-kai. Ka ce: Shi ne Allah Makadaici. Allah wanda ake nufinsa da bukata . Bai haifa ba , kuma ba a haife shi ba . " Kuma babu daya da ya kasance tamka a gare shi) .

 

2. Sannan ka ce: (Allahu Akbar) sai ka yi ruku'u, sannan ka ce:
(SUBHANA RABBIYAL AZIM).Kuma ana so ka maimaita fadar hakan.

 

3. Sannan sai ka dago daga ruku'u, sai ka ce alhalin kana tsaye: (SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAH).Sannan a ya yin da kashin bayanka ya mike sai ka ce: (RABBANA WALAKAL HAMDUH).

 

4. Sannan sai ka ce: (Allahu Akbar) daga nan sai ka tafi sujjada, ka ce alhalin kana mai sujjada (SUBHANA RABBIYAL A'ALA), Kuma ana so ka maimaita fadar hakan.

 

 

5. Sannan ka ce: (Allahu Akbar),sannan sai ka zauna, kuma sai ka ce:
(RABBIG FIR LIY), Kuma ana so ka maimaita fadar hakan.

 

 

6- Sannan ka ce: (Allahu Akbar). Sai ka yi sujjada, ka ce alhalin kana mai sujjada (SUBHANA RABBIYAL A'ALA), Kuma ana so ka maimaita fadar hakan.

 

 

7- Sannan ka ce: (Allahu Akbar). Sai ka ta shi domin yin raka'a ta biyu, sai ka aikata kamar yadda ka yi a raka'a ta farko.

    

 

8- Idan ka gama sujjada a raka'a ta biyu sai ka ce: (Allahu Akbar) sannan sai ka zauna domin ka karanta tahiya ta farko ita ce:

    

  Attahiyyatu Lillah, Wassalawatu wattayyibatu, Assalamu Alaika Ayyuhan-Nabiyyu wa rahmatullaahi wa barakatuh, As-Salamu Alaina wa ala ibadillahis-Saliheen. Ashhadu an La'ilaha illal Laahu, wa ashhadu anna Muhammadan Abduhu wa rasuluh.

Ma'ana: (Dukkan nau'in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi, da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne).

 

9- Idan sallar ta zamo mai raka'a biyu ce sai ka karashe abin da ake fada a tahiyar karshe kamar yadda bayanin sa zai zo nan gaba, sannan sai ka yi sallama. Idan kuma sallar ta kasance tana da raka'oI fiye da biyu sai ka tashi bayan ka gama tahiyar farko ka aikata abin da ka yi a raka'o'in da suka wuce.

10- A karshan sallah za ka ce:
(Allahu Akbar) sannan sai ka zauna, ka karanta tahiyar farko sannan ka kara da wannan:

  

Allahumma salli ala Muhammadin wa alaa ali Muhammadin kama sallaita alaa Ibrahima wa alaa ali Ibrahima Innaka Hameedun Majeed, Allahumma barik ala Muhammadin wa alaa ali muhammadin kama baarakta ala Ibrahima wa alaa ali Ibrahima Innaka Hameedun Majeed.

Ma'ana :Ya Allah,  ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga Ibrahimu da alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne, Mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu, da alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne, Mai girma).

11- Bayan ka gama tahiyar karshe sai ka ce:

Allahumma Rabbana Atina fid-Dunya hasanatan wa fil Akhirati hasanatan, Allahumma Inni A'uzu bika min Azabi Jahannama, wa min azabil Qabri, wamin fitnatil mahyaa wal mamaat, wamin fitnatil Masihil Dajjal.Ma'ana: (Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya, da kyakkyawa a lahira. Ya Allah,  Ina neman tsari da kai daga azabar jahannama, da azabar kabari, da fitinar rayuwa da ta mutuwa, da sharrin fitinar Dujal mai shafaffiyar albarka).

12- Bayan haka sai ka juya damanka sai ka ce:
(Assalamu alaikum wa rahmatullah).Sannan sai ka juya hagunka sai ka ce:
(Assalamu alaikum wa rahmatullah). 

  

 

Main Menu
This is Islam
Purity
Prayer
Five prayers
Question And Answer
 
Languages
العربية Arabic
انجليزي english
صيني china
كينى Kenya
نيبالي nip
ألماني grmany
تجالوج TAGALOG
بيساو Bisaya
كلقان Kalagan
هندى hindi
تاميلي tamil
السواسيلندية Swaziland
بنقالية bangal
فيتنامي vitnam
هوسا Hausa
اليابانية Japan
تركي torke
روسي rose
اسباني Español
كوري cory
أندونيسيا indonesia
لينغالا-كونغو LINGALA
رواندا raounda
برمجة و تطوير الموقع اكساء لتكنولوجيا المعلومات