.: Yanda ake yin tsarki :.
1- Ka wanke hannayenka da ruwa izuwa tsintsiyar hannu sau daya ko biyu ko uku.

2- Ka kurkure bakin ka sannan ka shaka ruwa sannan ka face sau daya ko biyu ko uku.

3- Ka wanke fuskarka sau daya ko biyu ko uku.

4- Ka wanke hannunka na dama sannan na hagu daga farkon tsintsiyar hannu zuwa dantse sau daya ko biyu ko uku.

5- Ka shafi kanka tare da kunnuwanka da ruwa.


6- Ka wanke kafarka ta dama sannan ta hagu izuwa idon sawu sau daya ko biyu ko uku.

|